Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council Kano-Nigeria
16.4K subscribers
160 photos
138 videos
18 files
860 links
Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council, Kano-Nigeria
Download Telegram
🎙️ RAMADAN⛓️TAFSIIR 🎙️
1443 (2022)
📼📼📼📼📼📼📼📼📼📼

Hausa

Rana Ta 27

28 - Ramadan - 1443 AH
(29-04-2022 CE)



Masallacin Sahaba Kundila Maiduguri Road, Kano-Nigeria

Tare Da:
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
Ku biyo mu ta Shafukanmu:

Facebook -

https://www.facebook.covcm/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/

Telegram Channel -

https://t.me/SMBUIPC

YouTube Channel -
https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg


🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

🕌 Islamic Propagation Council,
Kano
Karkashin Jagorancin:
Shaykh Muhammad Bin Uthman [HafizahuL-Laah]
=======================
WhatsApp
08065527420
09045421104
BAN KWANA DA RAMADAAN :

"وداعا لشهر البر والخير والبركة"
.
١- نرحب بالصيام لشهر خير*** نهاجر فيه شيطانا ذليلا
٢- أتانا الضيف شهرا للصيام***نصوم تعبدا ونقوم ليلا
٣-نرتل فيه تنزيل الكتاب **** بكل تخشع ركنا حصيلا
٤- به تتسابق الخيرات دوما*** سويعات كذا ليلا ok
٥- بذالك نبتغي حسن الختام*** لدى الجبار كان به كفيلا
٦- تكن في الغرب أمواج الفتون** ويأتي الصوم إنقاذا أصيلا
٧-وقد أزف الرحيل لضيف خير*** وكان قدومه حقا جميلا
٨- يغادرنا قضاء الله ربي**** رضينا لا نريد به بديلا
٩- أيا رمضان يا رمضان حبي*** تفارقني فكنت بذا هزيلا
١٠- تفارقني وشوق النفس تترى*** يسبب حسرة وكذا عويلا
١١- وداعا شهر إنفاق وخير**** وداعا كنت للتقوى دليلا
١٢-وليت الشعر هل أبقى لعام ** أصوم لديه رمضانا سبيلا
١٣-صلاة الله دوما والسلام *** على الهادي الذي عاب الرذيلا
Is
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وآله وصحبه وسلم
___
بقلم شيخنا:
الشيخ محمد بن عثمان
[حفظه الله]
🕌 KHUTBAH EID-UL-FITR 🕌
_________

Yau Litinin
01- Shawwal - 1443 A H
(02/05/2022 C E)



Daga:
Masallacin Sahaba Kundila Maiduguri Road, Kano

Tare Da:
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna wadannan links din dake kasa -

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/

Telegram Channel -

https://t.me/SMBUIPC

YouTube Channel -

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg


🕌 Islamic Propagation Council,
Kano
Karkashin Jagorancin:
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
======================
WhatsApp
08065527420
09045421104
🕌 KHUTBAH - JUMU'AH 🕌
_________

05 - 10 - 1443 AH
(06-05-2022 CE)

Mai Taken:
Alamomin Karbuwar Azumin Ramadaan
Daga:
Masallacin Sahaba Kundila Housing Estate, Maiduguri Road, Kano-Nigeria

Tare Da:
Dr. Abdullah Muhammad Getso
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna links din dake kasa -

Facebook-

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/


Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC

YouTube Channel:-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg

🕌 Islamic Propagation Council
Kano
Karkashin Jagorancin:
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
=======================
WhatsApp
08065527420
09045421104
INTERFAITH'), KURA DA FATAR RAGO!!

Shimfiɗa:
Da sunan Allah Mai rahamah Mai jinƙai. Tsira da Aminci su ƙara tabbata ga Manzon Allah, Iyalan gidanshi da kuma dukkanin Sahabbanshi haka ma waɗanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar ƙarshe.

Bayan haka:
Wannan 'yar maƙala tawa manufarta bayani ne kan:

✅ Me a ke nufi da "Interfaith"?

✅Mafarin harkar.

✅Tirƙa-tirƙa kan suna/ laƙabi

✅Hange da saƙo (Vision and mission)

✅Ƙarƙarewa

✅Kammalawa

❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️❇️

💠Me a ke nufi da ‘Interfaith’?

Wannan kalma tana da ɓangarori biyu: 'Inter' da kuma 'Faith'. Ita kalamar ‘inter’ wadda ta kan zo a matsayin 'tokarar baya' wato 'prefix' na nufin siffanta wani abu ne tsakanin ɓangarori guda biyu. Shi ya sa a misali, a ke cewa: 'International' wato tsakanin ƙasa da ƙasa ko 'lnter party' wato tsakanin jam'iyya da jam'iyya da sauransu. Wato ka ga saɓanin cewa 'intra' kenan. Wannan kuma ai kaga yana nufin ɓangare ɗaya ne kawai, abu ne na ckin gida, kamar kace 'intra party', wato al’amari da ya shafi cikin gida na wata jam’iyya. Ɗaya ɓangaren kuma shi ne sunan wato ita kalmar 'Faith. Kenan idan a ka ce 'Interfaith’ to siffantawa a ke nufi. Ma'ana wani al'amari ne TSAKANIN addinai ko kuma aƙidu. Idan kuma a ka ce
‘Inter party’ a na nufin alaƙa tsakanin jam'iyyoyi kenan. Haka dai haka dai...
💠Mafarin harkar:
Tun a shekarar 1893 (wato shekaru 129 kenan da suka wuce!), tun daga 11 zuwa 27 ga Satumba na dai ita wannan shekarar 1893 a wani zaure mai suna The Art Institute of Chicago a birnin Chicago da ke Jihar Illinois ta America a ka sa ɗigon ɗamba na ita wannan harka ta ‘Interfaith’. Daga cikin fitattun jagororin samar da tafiyar kuwa akwai wani mutum mai suna Charles Carrol Bonney
wanda a ka bayyana shi da cewa wani 'bagidaje' ne, wato 'layman'. Kuma dai shi wannan mutumin - Charles Carrol Bonney- shi ne wanda ya naɗa Henry Barrows -wani malamin Coci- a matsayin shugaban babban Kwamitin taron na 1893 a Chicago. Babban darakta na ita wannan tafiya a yanzu shi ne R̲e̲v̲. S̲t̲e̲p̲h̲e̲n̲ A̲v̲i̲n̲o̲. Wato Rabaran ne na Coci! Masana ƙeƙe da ƙaƙen abinda ke gudana game da wannan tafiya sun ce wannan taro shi ne na farko kuma jagaba wajen samar da kuma wanzar da ita wannan tafiya ta 'Interfaith' a tsare. To ka ga ashe da lauje cikin nadi, tunda asalin tafiyar ga inda ta fito. Haka yazo a wata maƙala a kan wannan taro mai kanun: Religion & Ethics Newsweekly, 23 October 2015.
Tsokaci:
Yau shekaru ɗari da ashirin da tara (129) kenan da fara wannan harka ta ‘Interfaith’ a duniya. Abin tambayar a anan shi ne: WANI ZAMAN LAFIYA, TSARO DA KWANCIYAR HANKALI HARKAR INTERFAITH TA KAWO MA MUSULMI A MATAKI NA DUNIYA (GLOBALLY) KO A MATAKI NA YANKIN AFIRKA (CONTINENTALLY) HAKA KUMA A MATAKI NA CIKIN ƘASA (NATIONALLY) KO MA A MATAKI NA TSUKI NA YANKI (LOCALLY)?
Wannan tambaya ya kamata a jefo ta saboda masu da'awar wai da ana irin wannan haɗuwar irin ta gambizar'Interfaith' wai da an daina samun rigingimu tsakanin Kirista da Musulmi. Ga adadin shekarun nan, amma har yanzu babu jini mafi arahar zubarwa yau a Duniya irin jinin Musulmi!!
Mun tsira a Filasɗinu da Kashmir da Iraq da Syria da Rohingya a ƙasar Myanmar?!
Mun tsira a yaƙin basasar tsohuwar Yugoslavia(Bosnia da Herzegovina)?. Su wa a kayi watandar rayuwarsu a Norway 22 ga July 2011 inda ɗan ta'adda Anders Behring Breivik ya kashe rayuka 77 mafi yawansu Musulmi?
Haka kuma menene laifin Musulmi 51 da ɗan Ta'adda Brenton Tarrant ya kashe ranar 15 ga Maris(March) 2019 a Masallacin An-Noor da ke Christchurch da kuma Linwood Islamic Center dukkaninsu a New Zealand?? Da sauransu da yawa.
Haka ma a nan gida Nigeria, su wa ake zalunta yawanci in ba Musulmi ba a fagage da dama?. (ko da yake sakacinmu yana da muni). Misali ƙwaya ɗaya: a Jihar Taraba, me ya hana ƴan 'Interfaith' ƙwato wa musulmi mafiya rinjaye haƙƙinsu na yin mulkin ita wannan Jihar ta hanyar lumanar tattaunawa domin ai ance"Democracy is a game of Number"?. Ai gashi nan a yanzu haka babu gawamna ɗaya Musulmi a Kudancin Nigeria in banda Gwamna Ishaq Gboyega Oyetola na Jihar Osun.
Su wa ke da rinjaye tsakanin Musulmi da Kirista a Lagos, Oyo, da Osun?
Abin fahimta dai shi ne Allah(SWT) Ya faɗa cewa:
وَلَن تَرْضَىٰ عَنكَ ٱلْيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ'
"Har abada Yahudawa da Nasara ba za su taɓa yarda da kai ba har sai ka bi hanyarsu (addininsu)" al-Baqarah:120
Ƙarƙashin fahimtar wannan Ayar ashe duk wanda ka ga Yahudu da Nasara da sauran munafukai suna yabonshi akan zaƙewarsa akan wannan harka ta 'Interfaith' ka san ya sauka daga turbar gaskiya.
Abin lura: Zaman tare cikin lumana da jituwa da kuma mutunta juna a ƙasa irin tamu ta Nigeria ya zama wajibi, tare da tattaunawa akan mas'aloli da suka shafi zamantakewa duk hakan babu laifi (muddin ba'a kaucewa dokokin Allah ba). Hakan kan zo ne domin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umma. Sai dai ba zai yiwu ba ne a shigo da wani shiri wanda ke ɗauke da lauje(ko ma barandami) cikin naɗi amma a lulluɓe shi da wani kirari ko suna mai jan hankali domin kaiwa ga wata manufa. Nan gaba kaɗan bayanin manufar zai bayyana- in shaa Allahu a gaɓar hange da saƙo(vision& mission)
💠Tirƙa tirƙa kan suna/laƙabi
Wasu na kiran harkar da suna 'Interfaith' wasu kuma suce/ 'Inter-religious', wasu su kuma cewa suke 'Interbelief' alhali kuma wasu na ce musu 'Interpath'. Wato dai kaga a nan sunaye ko laƙubba guda huɗu kenan amma duk na wani abu guda ɗaya. Kowa yana da mahangar da ya ke kallo wajen zaɓo waɗannan sunaye da laƙubba. Wasu ma sun ƙara da kiran haɗakar a matsayin wai haɗakar addinai masu bin aƙidar Annabi Ibrahim- 'alayhis Salaamu(Wato the Abrahamic faiths)!
Sun samu kansu cikin dawurwura da ɗimuwa dangane da suna da kuma laƙabi. Da farko, mu fara da shi wannan kirari na 'the Abrahamic faith' wato WAI gangamin addinai masu bin karantarwar Annabi Ibrahim-'alayhis Salaamu.
Hikimarsu da azancinsu a nan shi ne tunda addinin Musulunci da Kiristanci da kuma Yahudanci dukkaninsu suna da alaƙa da Annabin Allah Ibrahim 'alayhis Salaamu ta fuskar salsala da dangantakar jini, to yayi daidai a kira addinansu da wannan laƙabi 'Addinai Ibrahimawa' wato
'Abrahimic faiths'. Allah- 'Azza wa Jalla- tuni Ya ƙaryata wannan dangantaka muzayyafah. A cikni Suurah ta 3 aayah 67 da kuma ta 68
مَا كَانَ إِبْرَاهِيمُ يَهُودِيًّا وَلَا نَصْرَانِيًّا وَلَٰكِن كَانَ حَنِيفًا مُّسْلِمًا وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
إِنَّ أَوْلَى ٱلنَّاسِ بِإِبْرَٰهِيمَ لَلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ وَهَٰذَا ٱلنَّبِىُّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱللَّهُ وَلِىُّ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Ma'ana:
"Annabi Ibrahim ba bayahude ba ne ko banasare(Kirista) sai dai ya kasance mai karkata ne zuwa ga addinin gaskiya
kuma Musulmi, bai kasance daga cikin mushrikai ba"
A ayah ta gaba Allah Ya ce:
"Mafiya cancantar mutane da Ibrahim sune WAƊANDA SUKA BISHI DA KUMA WANNAN ANNABIN (Muhammad SAW) DA KUMA MASU IMANI..."
Ƙarara Allah Maɗaukaki Ya na kawar da waccan da'awar ta alaƙanta Annabi Ibrahim-'alayhis salaam- da da'awar addinai Ibrahimawa (the Abrahamic faiths). Dukkaninsu babu addinin da ke kan tsantsar tauhidin da Annabi Ibrahim 'alayhis Salaamu ya karantar in ba tantagaryar Musulunci ba.
Tafiya tai tafiya sai kuma wasu suka sake naɗa ma tafiyar wani sunan kuma wai shi 'Trialogue' , wato tattaunawar addinai uku kacal: Musulunci, Yahudanci da kuma Kiristanci. Irin wannan taron, fadar Vatican ta Fafaroma ta taɓa shirya irinshi a 1974, haka ma duk shekara a Bon Air ta Virginia ta America suna irin haka. Can kuma sai suka fahimci akwai matsala a sunan. Domin akwai waɗanda su ba sa bin ɗaya daga cikin dukkanin waɗannan addinan uku, misali ƴan Buddha da kuma addinin India wato Hinduism da kuma wasu addinan kamar su Zoroastrianism ja ka haɗa da irin su Jainism da sauransu.
Saboda haka sai suka sake yi wa sunan kwaskwarima. Suka ce domin a shigo da wasu addinan ya kamata a rinƙa kiran tattaunawar sa sunan 'Interreligious'. Wato haɗakar adinai Ka ga ta haka waɗannan addinan banda ukun farko duk sun samu shigowa kenan. Can kuma sai suka fahimci cewa ai akwai waɗanda su sam ba su ma da addinin. A gaskiya ma yaƙar kowane addini suke. Ga ire-iren waɗanda ake kira agnostics da atheists da irinsu humanists da sauransu.
Kuma duk su ma ana so a zauna lafiya da su!. Dan haka sai aka sake yi ma sunan gyran fuska, aka ce a rinƙa kiran haɗakar da suna 'inter-belief' ko kuma 'interpath'!Manufar dai ita ce wai dole kowa sai an tafi dashi kuma sai an gamsar da shi
Daga abinda ya gabata a wannan gaɓa, za'a fahimci kwamacala, bulkara da kuma ɗumasariya da ke tattare da harkar.
Gamsar da kowa da kowa tuƙewa ce da babu mai iya kaiwa gare ta
"إن إرضاء الناس غاية لا تُدرك

💠Hange da saƙo(Vision&mission)
Na ɗauko wannan 'Vision da Mission' ɗin ne daga shafin tushen wannan harkar mai wannan suna a ƙasa:
Interfaith Dialogue Forum

Ga abinda suka faɗa a shafinsu na farko lokacin da suke fayyace manufarsu da kuma inda suka sa gaba. Ga abinda suka ce:

Our Vision
"A world of peace, justice and sustainability"
Ma'ana: "(Samar da) duniya mai zama lafiya, adalci da ɗorewar haka ɗin"
Nace: Anya???!!!
Ina waɗannan abubuwan suke??

Our Mussion
"To cultivate harmony among the world’s religious and spiritual communities"
Ma'ana:"Samar da jituwa tsakanin addinan duniya da al'ummomi masu bin addinai"
Nace: Allah Ya tabbatar mana da alkhayri
"To foster their engagement with the world and its guiding institutions to address the critical issues of our time"
Ma'ana: "Ƙarfafa alaƙarsu(addinan) da tsarin duniya bisa bin dokokin da ke yi mata( ita duniyar) jagoranci"
Abin lura:
Daga bayanin nan nasu musamman"mission" ɗinsu wato saƙonsu, tambayoyi za su biyo baya:
1-Shin Musulunci shi ne zai bi tsarin da duniyar yau ke kai bisa dokokin da ke mata jagoranci?
2- Ko da dokokin sun saɓa ma karantarwar Musuluncin?
3- Namiji zai ɗauki kaso biyu na rabon mace a tsarin rabon gado(Q4:11). Shin tsarin duniyar yau ya yarda da wannan?
4- Wato kenan Musulmi su saki faɗin Allah-SubhaanaHU wa Ta'aala- domin bin saƙon iyayen Interfaith ƙarƙashin tsarin duniya?
5- Tsarin duniyar yau ya amince da sauya addini (riddah- wal 'iyaadhu bil Laahi!). Kowa ya san dokar Musulunci kan riddah. Shin menene iyayen 'Interfaith' suke nufi a nan
6- Kai Musulmi, wa za ka bi a nan? Mahaliccinka ko halittatu irinka?
7- Shin zai yiwu mutum ya saka kanshi cikin wannan harka ba tare da ya zama munafuki ba?!
8- Ya ɗan uwa/ ƴar uwa masu karatu, baku hango tambayoyi masu yawa kan wannan saƙon nasu ba?
9- Yaya za kayi da aayah ta 120 a Baƙarah: "Yahudu da Nasara ba za su taɓa yarda da kai ba har sai ka bi hanyarsu...? Haka kuma aayah ta 217 a dai cikin Baƙarah ɗin Allah Ta' aala Ya ce: "Ba za su gushe ba su na yaƙar ku har sai sun kautar da ku daga addininku idan suka samu dama...."

💠Ƙarƙarewa: Tattaunawa tsakanin Musulmi da masu bin wasu addinan musamman ma Kiristoci waɗanda muke tare kuma a haɗe a ƙasa ɗaya domin bayyana gaskiya ai haka ɗin wajibi ne. Allah Maɗaukaki a cikin aayah ta 64 cikin Surah ta uku yana cewa
:قُلْ يَٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَٰبِ تَعَالَوْاْ إِلَىٰ كَلِمَةٍۢ سَوَآءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشْرِكَ بِهِۦ شَيْـًٔا وَلَا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضًا أَرْبَابًا مِّن دُونِ ٱللَّهِ ۚ فَإِن تَوَلَّوْاْ فَقُولُواْ ٱشْهَدُواْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ
Fassara: "Ka ce ya ku waɗanda a ka baku littafi, ku taho zuwa ga wata kalmah madaidaiciya tsakaninmu da ku: Kada mu bauta ma wani in ba Allah ba, kada kuma mu haɗa SHI da komai wajen bauta kada kuma wani sashi namu ya mayar da wani sashen iyayen giji (abubuwan bauta) koma bayan Allah, idan sun bauɗe, to ku ce musu to ku sheda mu musulmi ne"
Manyan Malamai irinsu Ibnu Taymiyyah(RL) cikin al-Jawaabus Sahiih ya yi bayanai masu gamsarwa kan nuna ɓata irin ta Kirista. Haka ma almajirinshi Ibnul Qayyim cikin baitocinshi waɗanda suka fara da
…..أعباد المسيح لنا سؤال…. ya yi bayanai nagartattu kan haka.. da sauran malamai magabata ( RL).
Shaykh Ahmad Deedat- (RL) da irinsu Dr Zakir Abdul Karim Naik da kuma Dr Munqidh Saqqar ɗan ƙasar Syria da sauransu da yawa a wannan zamani suna ci gaba da bada gudunmowarsu a irin wannan fage.
Allah Maɗaukaki Ya faɗa a cikin littafinSHI Maigirma aayah ta 187 cikin surah ta 3 cewa:
{وَإِذْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثَاقَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ لَتُبَيِّنُنَّهُ لِلنَّاسِ وَلَا تَكْتُمُونَهُ فَنَبَذُوهُ وَرَاءَ ظُهُورِهِمْ وَاشْتَرَوْا بِهِ ثَمَنًا قَلِيلًا فَبِئْسَ مَا يَشْتَرُون
Fassara: "Kuma(ka tuna) lokacinda Allah Ya riƙi alƙawarin bauta na waɗanda aka basu littafi cewa: LALLAI LALLAI SAI KUN BAYYANA SHI GA MUTANE KADA KU ƁOYE SHI AMMA SAI SUKA YI FATALI DA SHI A BAYANSU SUNA MASU YIN CINIKINSHI DA WANI ƊAN ABIN DUNIYA , TIR DA ABINDA SUKE SAYOWA (Na halaka)."
Wannan nassi da ire-irenshi suna tabbatar da wajibcin bayyana ilimi da kuma haɗarin ɓoye shi ga waɗanda suka sani

💠 Kammalawa:
Wannan ɗan abinda ya sauƙaƙa kenan kan wannan mas'ala.

ALLAH KA NUNA MANA GASKIYA GASKIYA CE KUMA KA BAMU IKON AIKI DA ITA, KA KUMA NUNA MANA ƘARYA KARYA CE KUMA KA BAMU IKON GUJE MATA.

Wa sallal Laahu wa sallama wa baaraka 'alaa nibyyinaa Muhammadin wa'aalihii wa sahbihii aj'ma'iin

Daga: ✍🏻
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
🕌 KHUTBAH - JUMU'AH 🕌
_________

12 - 10 - 1443 AH
(13-05-2022 CE)

Abubuwan Da Khudbar Kunsa:
Falalar Jumu'ah, Ibadah , Siffofin Mai Neman Ilimi da Kuma Tsokaci Akan Wacce Ta Zagi Annabi (SAW)
Daga:
Garin Garko, Karamar Hukumar Garko, Kano-Nigeria

Tare Da:
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna links din dake kasa -

Facebook-

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/


Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC

YouTube Channel:-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg

🕌 Islamic Propagation Council,
Kano
Karkashin Jagorancin:
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
=======================
WhatsApp
08065527420
09045421104
Who is the actual causative agent for the ‘jungle Justice’: the provoker or the provoked? Why couldn’t the cause of the provocation be tolerant enough especially living within the community that firmly believes in the sanctity of the noble Prophet (SAW)??


✍
Shaykh Muhammad Bin Uthman
HafizahuL-Laah
Do you as - a Muslim- support an insult on our noble Prophet(SAW)?
I know your answer is NO
Then why talking ONLY on ‘jungle Justice’ to the detriment of the causative agent of the JJ? Can’t you-at least- be balanced?

Are you sincere here?


Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]