Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council Kano-Nigeria
16.4K subscribers
160 photos
138 videos
18 files
860 links
Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council, Kano-Nigeria
Download Telegram
Alhamdulillah, Alhamdulillah!

Muna godiya da fatan alkhayri da fatan kowa ya koma gida shi lafiya.

Mai girman Gwamna Engr. Alh Abba K Yusuf,
mun gode da wannan karamci da kayi mana,
Allah Ya saka da alkhayri.

Malamanmu, Attajirai da Sauran 'Yan Kasuwa, Iyayen Ƙasa, 'Yan Siyasa da Sauran al'umma.
Muna godiya ƙwarai da gaske.
Allah Ya sakawa kowa da alkhayri.
Da fatan an isa gida lafiya
🎙 AMSOSHIN 🎙
🔊 TAMBAYOYINKU
🎤🎤🎤🎤🎤🎤🎤

Tambaya:
Malam yayi nasiha ga Shugabannin saboda halin ƙunci rayuwa
- Ya halatta kasa ayi maka saukar al-Ƙur'ani saboda ƙuncin rayuwa;
- Su waye suka kashe Sayyidina Uthman (RA);
- Da Sauransu.

Tare Da:
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN [HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎

Don shiga shafikanmu:

Facebook-

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/

https://www.facebook.com/profile.php?id=100063489589432

Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC

YouTube Channel-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg
===================
WhatsApp
08065527420
Media is too big
VIEW IN TELEGRAM
Amsoshin Tambayoyinku

Tare Da:
Imaam Abuu Âsim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
FAƊAKARWA DA TUNATARWA:

KA YI MA KANKA AWO KAFIN A YI MAKA AWO.

Sayyiduna ‘Umar Bin al-Khattaab -رضي الله عنه- yana cewa:

“Ku yi ma kanku hisabi kafin ayi muku hisabi, ku auna ma kanku(ayyukanku) kafin a auna muku(a sikelin Ubangiji). Mafi sauƙin hisabi a gareku ranar tashin Ƙiyama shi ne ku fara yi ma kanku hisabi tun a nan duniya. Kuma ku shirya ma fuskantar ranar da za’a bijiro da ku a mafi girman rana ta bijirarwa, ranar da babu wata halitta mai iya ɓoyuwa(ko ɓoyewa)”

Matsayin wannan athar:

-Ahmad ya rawaito shi cikin الزهد shafi 120
- Abuu Nu’aymin shi ma haka cikin الحلية1/52
-Haka ma at-Tirmidhy ya ambace shi da siigha irin ta تمريض cikin Sunan ɗinshi 4/550 inda yake cewa …. ويُرْوى

A taƙaice dai wannan athari yana da ma’ana mai kyau amma yana da katsewa a jerin gwanon mazajenshi. Wannan katsewar (الانقطاع) kuwa ita ce tsakanin Thaabit Bin al-Hajjaaj da kuma ‘Umar Bin al-Khattaab رضي الله عنه

Haka ne ma yasa as-Shaykh Abuu Ishaaq al-Huwayny(H) ya ke cewa a cikin Takhriijinshi kan Tafsirin Ibn Kathiir:

وهذا سند رجاله ثقات لكنه منقطع بين ثابت بن الحجاج وعمر بن الخطاب فلم يدركه.ا. هـ. فالحاصل أن جميع طرق الأثر لا تثبت، والله أعلم

Allah Ya datar da mu.

____ ✍🏽
Imaam Abuu Âsim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahumuL-Laah]
BAKIN ZARE FA YA ƁACE MA AREWA- Bisa dukkanin alamu

MAFITA:

Mu koma zuwa ga Allah kacokan, zai yi mana kyautar rahamarSHI.
(dubo ayah 31 cikin Suurah 24)

Tabbataccen bincikenmu ya nuna mana cewa kwafe 30 na al-Qur'ani a ka jefa a masayi ko ƙazanta kuma a Arewa!!.
Har yanzu ɗin nan ni ban san wani mataki da a ka ɗauka (ko kuma dai muka ɗauka) ba a kan wanda yayi ko suka yi hakan.
An sha fa yin tarurruka na ƙoli(summits) kan haɓaka tattalin arzikin Arewa, kan lalaɓo bakin zare dangane da matsalar tsaro na Arewa da sauransu da sauransu. Duk waɗannan matakai ne masu kyau da kuma muhimmanci.
Amma tsaya. Shin an taɓa yin wani taro irin na ƙoli a Arewa..ina nufin Arewa tamu, ta mu Musulmi domin gano waɗanda suka yi wannan ta'asar?
Shin irin wannan kafircin bai kai ya tada hankalinmu ba ne?

Shifa tsaro Allah ne KAƊAI ke bada shi.

In an tsare dokokinSHI
sai YA bada tsaron, in ko ba haka ba sai YA bar mu da TSORO amma babu maganar TSARO
Karanta aayah 82 cikin Suurah 6:
الذين آمنوا ولم يلبسوا إيمانهم بظلم أولئك
لهم الأمن وهم مهتدون

Wannan fa ɗaya ne cikin bakunan zare da suka ɓace mana.

Allah gamu gareKA.

فالله المستعان وعليه
التكلان

------ ✍🏽
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]