Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council Kano-Nigeria
16.4K subscribers
160 photos
138 videos
18 files
860 links
Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council, Kano-Nigeria
Download Telegram
The whole issue is not about being in a New Year. On the contrary, it should be about turning a ’New Page’ in obeying Allah the Greatest and desisting from rebellious behavior against HIM. That should inform the actual meaning of being in ‘New Year’. This makes sense only for the discerning Souls, not the blindfolded.

___✍🏼
Abuu Asim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
The whole issue is not about being in a New Year. On the contrary, it should be about turning a ’New Page’ in obeying Allah the Greatest and desisting from rebellious behavior against HIM. That should inform the actual meaning of being in ‘New Year’. This makes sense only for the discerning Souls, not the blindfolded.

___✍🏼
Abuu Asim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
Saying “Happy or Merry Christmas” to a Christian is against the teachings of Islam. This is owing to the simple fact that you -as a Muslim- are happy about Jesus(AS) whom they claim to be Gad or son of Gad, being crucified!!!etc etc.
Are you not going against the clear teachings of the Glorious Qur’an? Read the GQ4:157 for more guidance
Haɗarin harshe da kuma muguwar magana- wani lokaci- sun fi yin ɓarna sama ɓarnar makami. Ɓarnar makami na iya warkewa amma mugun lafazi kan iya haifar da ɓarnar da ba ta da iyaka
JazaakaL-Laahu khayran Yaa Shaykhanaa
📚 KITAABUSH-SHIFAA'I 📚
_

Majlisi Na 07


12 - 07 - 1446  AH
(12-01-2025 CE)
                                                   Daga:
Masallacin Khalid Bin Walid, KSBS Street, Kundila Phase III, Zaria Road, Kano-Nigeria 
                    
                                 Tare Da:
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna links din dake kasa -

Facebook-

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/


Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC

YouTube Channel:-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg
====================
WhatsApp
08065527420
09045421104
JAN HANKALI/NUSARWA

Har yanzu a ƙasar Hausa, akwai wasu wurare da ‘ya’ya ke kiran sunayen iyayensu mata ƙarara ba tare da sayawa ba. Misali sai ka ji ɗa ko ‘ya na cewa: “Rahmatu ce ta aike ni ko Halima ce ta aike ni” - Yana gaya wa mahaifinshi kenan idan shi mahaifin yace: “ina za ka ko ina za ki”? Alhali kuma idan da ita mahaifiyar za ta tambaye shi/ta ina za ka/ki?, da kuwa ka ji sun ce: “Abba ne ko Baba ne ya aike ni” Abin tambayar a nan shi ne: Me yasa shi uba a ka ɓoye sunanshi domin girmamawa amma ita uwa aka bar nata sunan zanƙalƙal babu sakayawa ko sayawa iriin yanda aka yi ma shi uba? Kuma wani abin haushin shi ne sai kaga shi uban a gabanshi ‘ya’yan ke irin wannan rashin kyautawar amma ba ya kwaɓo! HABA UWA FA TA WUCE RAINI!! Ita fa (Uwa) haƙƙoƙi uku aka bata kafin aba uba haƙƙin biyayya sau ɗaya kamar yanda ya tabbata a Hadithin Manzo صلى الله عليه وآله وسلم Bukhari (5971) Muslim (2548)

Masu yi lallai a faɗaka kuma a faɗakar

_ ✍🏼
Abuu Âsim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
Faɗakarwar jijjifi (10)

A gaggauce:

1-In taƙamarka ilimi ne, ka tuna faɗin Allah a ayah ta 76 cikin Suratu Yuusuf:

“SAMA DA KOWANE MAI ILIMI AKWAI WANI MAI ILIMIN”

Haka kuma ayah ta 85 cikin Suratul Israa’i:

“KUMA BABU ABINDA A KA BAKU NA ILIMI FACE ƊAN KAƊAN”

2- In taƙamarka Mulki da sarauta ne, ka tuna faɗin Allah a ayah ta 54 cikin Suratun Nisaa’i:

“…LALLAI MUN BAI WA IYALAN GIDAN IBRAHIM LITTAFI DA HIKIMA KUMA MUN BASU MULKI MAI GIRMA”

Kai naka mulkin da kuma sarautar, Allah Ya kira ta maigirma?!!

3- In taƙamarka kuɗi ne, ka tuna faɗin Allah a ayah ta 76 cikin Suratul Qasas:

“KUMA MUN BASHI (wato Ƙaruna) TASKOKIN DUKIYA WAƊANDA MABUƊANSU NA WAHALAR DA DAKKAN MAZAJE (WAJEN ƊAUKA)”

Kaɗan ne cikin ire-iren waɗannanan saƙonnin daga littafin MAHALICCI.

Jiji da kai ba na mumini ba ne. GIRMAN KAI HARAMUN NE amma GIRMAMA KAI WAJIBI NE

____ ✍🏼
Abuu Asim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
🕌 KHUTBAH - JUMU'AH
____

https://chat.whatsapp.com/JNliyNDp4B46RKdEymNcbH


24 - 08 - 1446 AH
(24-01-2025 CE)

Khutbar ta ƙunshi bayanai dangane da abinda yake faruwa a Masjidus-Sahabah

Mai Taken:
Ka Guji Zalunci Don Kana Zaton Kana Da Ƙarfi
Daga:
Sabon Masallacin Jumu'ah Na Kundila, Maiduguri Road Kano-Nigeria

Tare Da:
Imaam Abuu Âsim
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna links din dake kasa -

Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC


Facebook-

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/


YouTube Channel:-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg
===================
WhatsApp
08065527420
Waƙe Kenan Da Aka Rerawa Shaykhana Shaykh Muhammad Bin Uthman. Allaah Ya tsare Mana kai Shaykhana

#Limamin_Kundila
👳🏻‍♂️🎤🔊
Ka daɗe a fage na gyãra
Ba ka yin zagi da kyãra
Ka ƙware a hali na kãra
Ga damo bai ta da ƙura

Shekaru ashirin da ɗori
Ka buwayi su o'o bori
Masu ɓata gari da tsãri
Ayyukansu su yaɗa sharri

Ƙoƙarin da ka yo a bãya
Shi suke burin su sauya
Sun gaza, Allah Ya juya
Sharruka bisa kansu, gayya!

Ran ƙiyama ta kusanto
Tun da bayi sun zamanto
Masu zalunci da runto
In ka so ka kira su ƙwarto

Ka yi dattako na sunna
Yaudara suka yo da ɓarna
Babu kunya sun yi murna
Mun ga dattako ka nuna

Masu makirci da gãba
Sun yi sun gaji babu riba
Kunyata, hau za su ɗiba
Babu ƙima babu haiba

Duk da tinƙaho na kifi
Ba ya kwana sai a rãfi
In ya kuskura zai ji zãfi
Na wuƙarmu tana da kaifi

Shehi tun kafin su wãye
Ka yi nisa gun kiranye
Ga miyagu, don su janye
Lafiya lau zã ka wanye

#Sadiq (Abu_Ahlãm) ✍️
26/01/2025
Gaskiya Sunan ta Gaskiya
Kuma Guda Daya ce:

Mu muna yaƙar zalunci da kuma waɗanda suka yi, akan Sabon Masallacin Kundila

Alhamdulillah
Allah Yasa al'umma suna fahimtar me ake ciki kuma menene yake faruwa. Wannan ma ƙarin nasara ce.
Ɗan bayanin da Shaykhanaa yayi akan batun Ranar Jumu'ah akan Mumbari da kuma bayanan da yayi da 'Yan Jaridu, lallai masu hankali daga cikin wannan al'umma sun tabbatar da cewa da akwai makirci da zalunci a cikin al'amarin.

Zamu cigaba da fito da abubuwan kamar yadda suke in shaa Allahu, idan da buƙatar kuma a ambaci suna zamu ambata ko sunan wanene don babu wanda muke jin tsoro.
Shi wancan gwanin zancen, sakataren masallacin da yazo kare Maigidan shi a ranar bayan gama sallah, ya kama wasu sunaye don ya wanke su amma bana jin sun wanku, watakila ma datti ya watsa musu.

Muna roƙon Allah Ya bayyana mana gaskiyar
Allah Ya cigaba da kare mana Malaminmu, Shugabanmu kuma Jagoranmu -Shaykh Muhammad Bin Uthman [HafizahuL-Laah]
"Lallai A Cikin Haka Akwai Abun Lura Ga Ma'abota Hankali Da Basira..."

Sun yi tambaya: Wai -"...Yanzu Malam mai kake so ayi?" Sai Malam yace: "...a'a ku za a tambaya, me yasa kuka yi abinda kuka yi?"

Shin wai menene laifin Malam da yasa aka yi masa haka?
Masallacin ne yayi masa girma ko kuwa matsayin shine bai isa ya riƙe jagorancin Masallacin ba?
Su Malaman da aka gayyato cikin harkar Masallacin da akwai wata tuhuma da suke yiwa Malam ne?
Dukkan su suna da nasu Masallatan da Cibiyoyi da suke riƙewa kuma sune suke jagoranci da gudanar da al'amuran Cibiyoyin su. Da akwai wanda zai aminta da irin wannan a wajen shi?
Menene laifin da Malam yayi musu, wanda suka kasa fitowa su faɗa kuma suke ganin ba zasu iya mara masa baya a yaƙi zaluncin da akayi mashi ba?

Har yanzu muna cewa idan bayanan da Shaykhanaa yayi ba haka suke ba. Don Allah ku fito ku faɗi inda ba haka bane. Idan kuma akayi shiru. Yin shirunku yana tabbatar da bayanan shi dai dai ne. Kuma kenan son zuciya aka bi da ƙin jinin Malam watakila ma har da hassada.

Daga ranar da aka ambaci sunayen ku don ana neman a wanke ku, zuwa yau kuyi nazari ku gani, daraja ce ko akasin haka?

Mu a bangarenmu wannan ƙarin ɗaukaka ce ga Malaminmu. Kuma ko a haka aka tsaya....

Allah mun gode
Allah Ka ƙara kare mana Malaminmu Jagoran mu
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
RIGAKAFI: ZAI ZAMA TSANTSAR GAZAWA IDAN MAJALISAR MALAMAN KANO SUKA UMARCI BIN-UTHMAN YA CIGABA DA SALLAH A TSOHON MASALLACINSA DOMIN ANZO GABAR DA ZASUYI ADALCHI IDAN SU NA BUKATAR YIN ADALCHIN.

Assalamu alaikum

Jiya naji Jawabin babban Malami Sheikh Ibrahim Khalil game da takaddama da akeyi akan sabon Masallacin Juma'a na Kundila da kuma Sheikh Muhammad Bin-Uthman.

A hirar da a kayi da Malam. Ibrahim Khalil Na fahimci abubuwa dayawa a hirar amman dai rigakafin da zamuyi shine "ZAI ZAMA TSANTSAR GAZAWA IDAN MAJALISAR MALAMAN KANO SUKA UMARCI BIN-UTHMAN YA CIGABA DA SALLAH A TSOHON MASALLACINSA DOMIN ANZO GABAR DA ZASUYI ADALCHI IDAN SU NA BUKATAR YIN ADALCHINADALCHIN".

GA DALILAINA NA YIN WANNAN RUBUTUN

1. Sheikh Muhammad Bin-Uthman ya aminta da Majalisar Malaman Jahar Kano.

2. Bangaren Mai Kifi suma sun amince da Majalisar Malaman Jahar Kano.

ME AKE NUFI DA ADALCHI

Adalchi shine yin hukunci daidai da abunda aka aikata. Misali idan na Mari Mutum a Mare ni, idan ka kashe Mutum a kashe ka, idan kayi sata da yakai ayi maka haddi a yanke maka hannu. Idan kayi zina baka da aure ayi maka bulala 100 idan kayi Qazafi kuma ba shaida ayi maka bulala 80. Haka naji Malamai suke fada suke kafa mana hujja da Qur'ani da Hadith.

ABUBUWAN DA NAKE BAWA MAJALISAR MALAMAN JAHAR KANO SHAWARA DASU DUBA SUNE.

1. Shin Mai Kifi yayiwa Tsohon masallacin Sahaba alkawari zai gina musu sabo?

2. Shin lokacin da Sheikh Bin-Uthman yake ta addua da ziyartar wannan aiki Alh. Adamu ya taba dakatar dashi?

3. Sati daya kafun abude sabon Masallaci nayi Sallah a Sahaba naji Malam Bin-Uthman yayi sanarwar za'a koma sabon Masallaci shin Mai Kifi ya sanar dashi cewa ba ku na ginawa ba?

4. Shin da gaske ne lokacin da ake wannan gini an saka Sunan MASJIDUS SAHABA a SIGN BOARD "PROPOSED SAHABA JUMA'AT MOSQUE"?

5. Shin Mai Kifi Limanci yakeso ko kawai taimako yake yakeso yake bayarwa?

6. Shin tsohon masallacin Sahaba bashi da Kwamitin gudanarwane?

7. Sabbin Limamai da aka kawo wannan masallacin basu da masallacinsu ne?

DAGA KARSHE

1. Majalisar Malamai kuji tsoron Allah domin Mai Kifi ba Limanci yakeso ba.

2. Kuji tsoron Allah kada Ku Kara raba kan al'ummar musulmai ta hanyar dasa gaba da kiyayya tsakanin dalibansu da Malamansu.

MUNA ADDU'AR ALLAH YAYI RUKO DA HANNAYENKU YAKUMA BAKU DAMAN YIN HUKUNCIN DA ZAI HADA KAN AL'UMMAR MUSULMAI. ALLAH YAKARE KU DAGA FADAWA CIKIN SON ZUCIYA.

Hon. Bashir Dalhatu
Kauyen Alu
2nd February, 2025.