Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council Kano-Nigeria
16.4K subscribers
160 photos
138 videos
18 files
860 links
Shaykh Muhammad Bin Uthman - Islamic Propagation Council, Kano-Nigeria
Download Telegram
Faɗakarwar jijjifi (10)

A gaggauce:

1-In taƙamarka ilimi ne, ka tuna faɗin Allah a ayah ta 76 cikin Suratu Yuusuf:

“SAMA DA KOWANE MAI ILIMI AKWAI WANI MAI ILIMIN”

Haka kuma ayah ta 85 cikin Suratul Israa’i:

“KUMA BABU ABINDA A KA BAKU NA ILIMI FACE ƊAN KAƊAN”

2- In taƙamarka Mulki da sarauta ne, ka tuna faɗin Allah a ayah ta 54 cikin Suratun Nisaa’i:

“…LALLAI MUN BAI WA IYALAN GIDAN IBRAHIM LITTAFI DA HIKIMA KUMA MUN BASU MULKI MAI GIRMA”

Kai naka mulkin da kuma sarautar, Allah Ya kira ta maigirma?!!

3- In taƙamarka kuɗi ne, ka tuna faɗin Allah a ayah ta 76 cikin Suratul Qasas:

“KUMA MUN BASHI (wato Ƙaruna) TASKOKIN DUKIYA WAƊANDA MABUƊANSU NA WAHALAR DA DAKKAN MAZAJE (WAJEN ƊAUKA)”

Kaɗan ne cikin ire-iren waɗannanan saƙonnin daga littafin MAHALICCI.

Jiji da kai ba na mumini ba ne. GIRMAN KAI HARAMUN NE amma GIRMAMA KAI WAJIBI NE

____ ✍🏼
Abuu Asim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
🕌 KHUTBAH - JUMU'AH
____

https://chat.whatsapp.com/JNliyNDp4B46RKdEymNcbH


24 - 08 - 1446 AH
(24-01-2025 CE)

Khutbar ta ƙunshi bayanai dangane da abinda yake faruwa a Masjidus-Sahabah

Mai Taken:
Ka Guji Zalunci Don Kana Zaton Kana Da Ƙarfi
Daga:
Sabon Masallacin Jumu'ah Na Kundila, Maiduguri Road Kano-Nigeria

Tare Da:
Imaam Abuu Âsim
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna links din dake kasa -

Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC


Facebook-

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/


YouTube Channel:-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg
===================
WhatsApp
08065527420
Waƙe Kenan Da Aka Rerawa Shaykhana Shaykh Muhammad Bin Uthman. Allaah Ya tsare Mana kai Shaykhana

#Limamin_Kundila
👳🏻‍♂️🎤🔊
Ka daɗe a fage na gyãra
Ba ka yin zagi da kyãra
Ka ƙware a hali na kãra
Ga damo bai ta da ƙura

Shekaru ashirin da ɗori
Ka buwayi su o'o bori
Masu ɓata gari da tsãri
Ayyukansu su yaɗa sharri

Ƙoƙarin da ka yo a bãya
Shi suke burin su sauya
Sun gaza, Allah Ya juya
Sharruka bisa kansu, gayya!

Ran ƙiyama ta kusanto
Tun da bayi sun zamanto
Masu zalunci da runto
In ka so ka kira su ƙwarto

Ka yi dattako na sunna
Yaudara suka yo da ɓarna
Babu kunya sun yi murna
Mun ga dattako ka nuna

Masu makirci da gãba
Sun yi sun gaji babu riba
Kunyata, hau za su ɗiba
Babu ƙima babu haiba

Duk da tinƙaho na kifi
Ba ya kwana sai a rãfi
In ya kuskura zai ji zãfi
Na wuƙarmu tana da kaifi

Shehi tun kafin su wãye
Ka yi nisa gun kiranye
Ga miyagu, don su janye
Lafiya lau zã ka wanye

#Sadiq (Abu_Ahlãm) ✍️
26/01/2025
Gaskiya Sunan ta Gaskiya
Kuma Guda Daya ce:

Mu muna yaƙar zalunci da kuma waɗanda suka yi, akan Sabon Masallacin Kundila

Alhamdulillah
Allah Yasa al'umma suna fahimtar me ake ciki kuma menene yake faruwa. Wannan ma ƙarin nasara ce.
Ɗan bayanin da Shaykhanaa yayi akan batun Ranar Jumu'ah akan Mumbari da kuma bayanan da yayi da 'Yan Jaridu, lallai masu hankali daga cikin wannan al'umma sun tabbatar da cewa da akwai makirci da zalunci a cikin al'amarin.

Zamu cigaba da fito da abubuwan kamar yadda suke in shaa Allahu, idan da buƙatar kuma a ambaci suna zamu ambata ko sunan wanene don babu wanda muke jin tsoro.
Shi wancan gwanin zancen, sakataren masallacin da yazo kare Maigidan shi a ranar bayan gama sallah, ya kama wasu sunaye don ya wanke su amma bana jin sun wanku, watakila ma datti ya watsa musu.

Muna roƙon Allah Ya bayyana mana gaskiyar
Allah Ya cigaba da kare mana Malaminmu, Shugabanmu kuma Jagoranmu -Shaykh Muhammad Bin Uthman [HafizahuL-Laah]
"Lallai A Cikin Haka Akwai Abun Lura Ga Ma'abota Hankali Da Basira..."

Sun yi tambaya: Wai -"...Yanzu Malam mai kake so ayi?" Sai Malam yace: "...a'a ku za a tambaya, me yasa kuka yi abinda kuka yi?"

Shin wai menene laifin Malam da yasa aka yi masa haka?
Masallacin ne yayi masa girma ko kuwa matsayin shine bai isa ya riƙe jagorancin Masallacin ba?
Su Malaman da aka gayyato cikin harkar Masallacin da akwai wata tuhuma da suke yiwa Malam ne?
Dukkan su suna da nasu Masallatan da Cibiyoyi da suke riƙewa kuma sune suke jagoranci da gudanar da al'amuran Cibiyoyin su. Da akwai wanda zai aminta da irin wannan a wajen shi?
Menene laifin da Malam yayi musu, wanda suka kasa fitowa su faɗa kuma suke ganin ba zasu iya mara masa baya a yaƙi zaluncin da akayi mashi ba?

Har yanzu muna cewa idan bayanan da Shaykhanaa yayi ba haka suke ba. Don Allah ku fito ku faɗi inda ba haka bane. Idan kuma akayi shiru. Yin shirunku yana tabbatar da bayanan shi dai dai ne. Kuma kenan son zuciya aka bi da ƙin jinin Malam watakila ma har da hassada.

Daga ranar da aka ambaci sunayen ku don ana neman a wanke ku, zuwa yau kuyi nazari ku gani, daraja ce ko akasin haka?

Mu a bangarenmu wannan ƙarin ɗaukaka ce ga Malaminmu. Kuma ko a haka aka tsaya....

Allah mun gode
Allah Ka ƙara kare mana Malaminmu Jagoran mu
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]
RIGAKAFI: ZAI ZAMA TSANTSAR GAZAWA IDAN MAJALISAR MALAMAN KANO SUKA UMARCI BIN-UTHMAN YA CIGABA DA SALLAH A TSOHON MASALLACINSA DOMIN ANZO GABAR DA ZASUYI ADALCHI IDAN SU NA BUKATAR YIN ADALCHIN.

Assalamu alaikum

Jiya naji Jawabin babban Malami Sheikh Ibrahim Khalil game da takaddama da akeyi akan sabon Masallacin Juma'a na Kundila da kuma Sheikh Muhammad Bin-Uthman.

A hirar da a kayi da Malam. Ibrahim Khalil Na fahimci abubuwa dayawa a hirar amman dai rigakafin da zamuyi shine "ZAI ZAMA TSANTSAR GAZAWA IDAN MAJALISAR MALAMAN KANO SUKA UMARCI BIN-UTHMAN YA CIGABA DA SALLAH A TSOHON MASALLACINSA DOMIN ANZO GABAR DA ZASUYI ADALCHI IDAN SU NA BUKATAR YIN ADALCHINADALCHIN".

GA DALILAINA NA YIN WANNAN RUBUTUN

1. Sheikh Muhammad Bin-Uthman ya aminta da Majalisar Malaman Jahar Kano.

2. Bangaren Mai Kifi suma sun amince da Majalisar Malaman Jahar Kano.

ME AKE NUFI DA ADALCHI

Adalchi shine yin hukunci daidai da abunda aka aikata. Misali idan na Mari Mutum a Mare ni, idan ka kashe Mutum a kashe ka, idan kayi sata da yakai ayi maka haddi a yanke maka hannu. Idan kayi zina baka da aure ayi maka bulala 100 idan kayi Qazafi kuma ba shaida ayi maka bulala 80. Haka naji Malamai suke fada suke kafa mana hujja da Qur'ani da Hadith.

ABUBUWAN DA NAKE BAWA MAJALISAR MALAMAN JAHAR KANO SHAWARA DASU DUBA SUNE.

1. Shin Mai Kifi yayiwa Tsohon masallacin Sahaba alkawari zai gina musu sabo?

2. Shin lokacin da Sheikh Bin-Uthman yake ta addua da ziyartar wannan aiki Alh. Adamu ya taba dakatar dashi?

3. Sati daya kafun abude sabon Masallaci nayi Sallah a Sahaba naji Malam Bin-Uthman yayi sanarwar za'a koma sabon Masallaci shin Mai Kifi ya sanar dashi cewa ba ku na ginawa ba?

4. Shin da gaske ne lokacin da ake wannan gini an saka Sunan MASJIDUS SAHABA a SIGN BOARD "PROPOSED SAHABA JUMA'AT MOSQUE"?

5. Shin Mai Kifi Limanci yakeso ko kawai taimako yake yakeso yake bayarwa?

6. Shin tsohon masallacin Sahaba bashi da Kwamitin gudanarwane?

7. Sabbin Limamai da aka kawo wannan masallacin basu da masallacinsu ne?

DAGA KARSHE

1. Majalisar Malamai kuji tsoron Allah domin Mai Kifi ba Limanci yakeso ba.

2. Kuji tsoron Allah kada Ku Kara raba kan al'ummar musulmai ta hanyar dasa gaba da kiyayya tsakanin dalibansu da Malamansu.

MUNA ADDU'AR ALLAH YAYI RUKO DA HANNAYENKU YAKUMA BAKU DAMAN YIN HUKUNCIN DA ZAI HADA KAN AL'UMMAR MUSULMAI. ALLAH YAKARE KU DAGA FADAWA CIKIN SON ZUCIYA.

Hon. Bashir Dalhatu
Kauyen Alu
2nd February, 2025.
Haƙuri Mai Tadda Rabo -"Duk wanda ya dogara ga Allah, Allah Zai bashi mafita..."

-IDANUWA AKAN MAJALISAR MALAMAI

Kamar yadda bayanai suka gabata, Malaminmu Shaykhanaa Shaykh Muhammad Bin Uthman, ya tattara komai ya miƙawa Majalisar Malamai (Council Of Ulama) don suyi duba a cikin wannan al'amari na dambarwar Sabon Masallacin Kundila.
Akan haka Malam yake nusar da 'Yan-uwa da ayi haƙuri a 'mayar da wuƙa cikin kube' a saurari abinda wannan Majalisa zata fito da shi.

Shaykhanaa, mutum ne mai haƙuri da kawaici da kuma bin abubuwa a hankali cikin natsuwa, a lokaci guda kuma yana da jajircewa wajen sai gaskiya ta fito kuma an tafi a kan ta. Shi yasa mafi yawan lokaci yakan yi addu'ar "Ya Allah Ka nuna mana gaskiya, gaskiya ce, Ka azurta mu da bin ta. Ka kuma nuna mana ƙarya, ƙarya ce Ka azurta mu da guje mata".

Bamu da masaniya akan wannan Majalisa ta Malamai, shin maslaha zata yi, ko shawara zata bayar, ko hukunci zata yi ko kuwa umarni zata bayar. Allah Ne mafi sani. Amma dai muna sauraro.

Muna bada shawara ga Majalisar Malamai da ta dubi Allah ta fito da abinda yake adalci ne kamar yadda muke kyautata mata zato. Don hakan ya zama kwanciyar hankali, ya zama aminci ita kuma Majalisa ya zama mata waraka da samun aminci da nutsuwa daga wajen al'umma.

Dukkan 'Yan-uwa da Masoya da kuma magoya baya ga Shaykhanaa, Shaykh Muhammad Bin Uthman mun zuba ido ga makomar Majalisar Malamai a wannan batu. Bana jin idan aka shigo da son zuciya cikin wannan al'amari zamu iya samun nutsuwa bare kuma har akai matakin mu karɓa mu sallama. Wanda bama fatan hakan.

Muna yiwa kowa fatan alkhayri tare da godiya mai yawa ga soyayya da fatan alkhayri da 'Yan-uwa suke nunawa wannan Jagora namu Shaykh Muhammad Bin Uthman [HafizahuL-Laah].
Allah Ya ƙara ɗaukaka mana shi, Ya tsare mana shi, Ya kare mana shi daga sharrin duk wani abin halitta. Allah Ya ƙarawa rayuwar shi albarka.
Allah Yasa mu gama lafiya -aamiin Yaa Allaah.
_
Salisu Ibrahim
Secretary
IPC Kano
SARA DA SASSAƘA BASA HANA GAMJI TOHO...!!

Shaykhanaa Shaykh Muhammad Bin Uthman Ya Zama Gwal "Ana Ƙara Ƙona Shi Yana Ƙara Ƙyalli Da Sheƙi."

Wani Wai Shi Imam Aliyu Indabawa
Ya fito yana bayyana kan shi da kuma nuna jahilcin shi akan abinda kodai bai sani ba ko kuma anyi mashi 'ingiza mai kantu ruwa'
Kamata yayi ya koma a sake masa karatun ko kuma waɗanda suka turo su jawo masa. Don mun fahimci ina ya dosa.

AY Maikifi ne ya faɗa maka cewa bai yi magana da Malam akan Sabon Masallacin ba ko kuwa ƙarya kake yi masa?

Wanene ya baka labarin dangane da Kotu kuwa da kai aka je Kotun?

Duk wanda yace har da AY Maikifi aka Kai ƙara a farkon sammacin da Kotu ta kawo, ko waye ƙarya yake yi. A cikin biyar ɗin da Kotu ta sanar a farko babu Maikifi a ciki duk wanda yake a lokacin ya san haka.
A zaman farko a Kotu wasu lawyoyi suka tashi suka ce, su suna wakiltar AY Maikifi ne suna son wannan Kotu ta shigar da shi cikin waɗanda ake ƙara. Kotu kuma ta amsa musu ta karɓi buƙatarsu. Kaji inda AY Maikifi ya shigo ciki.

Sannan a ƙaryar da yayi, yace wai Malam da Masallacin Sahaba basu dauki lauya ba. Kaga wannan ya tabbatar cewa harmagaza yake yi, babu abinda ya sani, don bai halarci Kotu ba, wanda ya turo shi bai san komai a zaman kotu. Don kuwa da sun halarci zaman to da sun ga taron lauyoyi.

Yanzu kai Imam Indabawa mun gane ka. Wai har kana cewa Shaykh Muhammad Bin Uthman Malaminka, a a kadai sake magana, ko kuwa kana faɗa ne don mu yarda da kai. Wannan ma ai ba mai yiwuwa bane.

Muna nan muna jiran ire-irenku da kuma masu turo ku, kuna burma wa kan ku wuka a ciki.

Allah zai bayyana mana ku ɗaya bayan ɗaya in shaa Allahu.

Allah Ya ƙara kare mana Malaminmu kuma muna fata Allah Ya dawo mana da shi lafiya.

_ ✍🏼
Salisu Ibrahim
Secretary
IPCKano
Idan Fitsari Banza Ne, Kaza Ma Tayi...!
Sako ne zuwa ga Imam Aliyu Indabawa -

Shaykhanaa, Shaykh Muhammad Bin Uthman, International ne a fagen Da'wah.
Kaji da kyau!
Ko kuwa shi MC da 'Ana-Saki-Kana-Tarewa' basu fahimta bane?!
Ko kuwa a cikin karatun da aka biya maka, wanda ka kasa abin kirki, sai ƙara 'kwance musu zani a kasuwa'. Kai ne kazo kayi musu kari a ciki?

Malam International Scholar ne, babu shakka akan wannan. Mun faɗa Malaminmu, Jagoranmu International ne.
Idan Fitsari Banza ne Kaza ma tayi mana.

Kaje ka fadawa MC naka mun ce a faɗa mashi Shaykh Muhammad Bin Uthman International ne
Ka kuma je ka faɗawa 'Ana-Saki-Kana-Tarewa' mun ce a faɗa mashi Shaykh Muhammad Bin Uthman International ne.

Duk lokacin da kuka yi magana akan shi sai kuma da darajar shi su ƙara ɗagawa
Alhamdulillah wannan Allah Ne Yake yi.

Yaa Allah Ka ƙara daraja da ɗaukaka ga wannan Bawan naKa Malaminmu Shugabanmu kuma Jagoranmu
Shayk Muhammad Bin Uthman
Yaa Allaah Ka ƙara kare mana shi -aamiin thumma aamiin

___
Salisu Ibrahim
Secretary
IPCKANO
*DA'WAH CONFERENCE A ƘASAR UGANDA*

Allah Yasa a gama Taro lafiya Ya maido mana da kai gida lafiya -aamiin
TSOKACI AKAN WADANSU MAS'ALOLI MASU MUHIMMANCI

1. Gado;
2. Riba;
3. Aure.

Tare Da:
Shaykhanaa
Abuu Âsim
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]

Allaah Ya saka masa da alkhayri -aamiin

👇🏾👇🏾
Audio
Audio from Salisu Ibrahim
Audio
Audio from Salisu Ibrahim
https://www.facebook.com/share/p/18Rq2YLkZs/


Lecture Delivered by:
Imam Abu Asim Shaykh Muhammad bin Uthman
[HafizahuL-Laah]

At UGANDA

TOPIC:
Addressing Misconception on Islamic Morality.
🕌 KHUTBAH - JUMU'AH
_

14 - 08 - 1446 AH
(14-02-2025 CE)

Mai Taken:
Cin Amfanin Biyar Kafin Biyar
Daga:
Masallacin Government College Kaduna-Nigeria

Tare Da:
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN
[HafizahuL-Laah]
💎💎💎💎💎💎💎

Don Shiga Shafukanmu danna links din dake kasa -

Telegram Channel-

https://t.me/SMBUIPC


Facebook-

https://www.facebook.com/groups/2111965292215806/

https://www.facebook.com/Shaykh-Muhammad-Bin-Uthman-Islamic-Propagation-Council-Kano-Nigeria-2598939453511089/


YouTube Channel:-

https://www.youtube.com/channel/UC5uls8-ZZu60AD3jAkphgvg
===================
WhatsApp
08065527420