TARBIYYAH RAMADAANIYYAH
A cikin wani hadiithi(Qudsy) Manzon Allah-صلى الله عليه وآله وسلم yana cewa-bisa riwayar Abii Hurayrah- RA:
Allah Mai buwaya da bunƙasa yana cewa:
“Dukkanin aikin ɗan Adam nashi ne in banda azumi, shi wannan nawa ne kuma NI NE KE BADA SAKAMAKO A KAN SHI. Idan lokacin azumin ɗayanku yayi, to kada yayi batsa kuma kada yayi hargowa(hayagaga). Idan ma wani ya zage shi ko ya yaƙe shi, to yace ni mutum ne mai azum. Na rantse da WANDA rayuwar Muhammad ke hannunSHI, bashin bakin mai azumi shi yafi ƙamsasuwa a wajen Allah sama da ƙamshin al-Miski. Mai azumi yana da aji biyu na farin ciki da zai samu morewa da su: 1- Idan yazo buɗabaki zai yi farin ciki haka kuma 2- Lokacin haɗuwa da Ubangijinshi, zai farin ciki a dalilin azuminshi”
Fitarwar al-Imamul Bukhary cikin Sahiih ɗinshi (1904) haka shi ma al-Imamu Muslim (1151) tare da ɗan bambanci kaɗan.
Tirƙashi!! Waɗannan karamomin da martabobin, da kuma dangogi na falalar, mai azumi Na gaskiya ne fa kawai zai same su.
_
Shaykh Muhammad Bin Uthman
[HafizahuL-Laah]