WAHA HAUSA (Labaran hauzar Najaf al-ashraf)
Photo
Babban Marja'in Addini Sheikh Muhammad Al-Yaƙubi (Allah Ya dawwamar da inuwarsa) ya ce: Afirka ita ce matattarar Musulunci ta farko bayan Makka... Kuma ɗaliban ilimin addini suna da alhakin isar da saƙon Ahlul Baiti (a.s.) zuwa duniya baki ɗaya
16 Safar 1448H / 31-07-2026
Marja'in Addini musulunci Ayatullah Sheikh Muhammad al-Yaƙuby (Allah Ya dawwamar da inuwarsa) ya tabbatar da cewa nahiyar Afirka ita ce matattarar Musulunci ta farko bayan Makka Mai Alfarma, domin ita ce ta karɓi bakuncin musulmai na farko da suka yi hijira domin tsira da addininsu daga zalunci da tsanantawar Ƙuraishawa. Ya kuma yi kira ga ɗaliban ilimin addini na Afirka da su yi amfani da wannan dangantaka mai zurfin tarihi wajen ɗaukar saƙon Musulunci mai girma da kuma yaɗa koyarwar Ahlul Baiti (a.s.) a sassa daban-daban na duniya.
Hakan ya zo ne cikin wani bayani da ya gabatar a ofishinsa da ke birnin Najaf Ashraf a gaban taron ɗalibai maza da mata 'yan Afirka masu karatu a Hauzar Ilimi ta birnin Qum mai tsarki. A cikin jawabinsa, Shehin malamin ya yi bayani kan tushen dangantakar tarihi mai ƙarfi tsakanin nahiyar Afirka da Musulunci, yana mai bayyana cewa hijirar farko zuwa Habasha ita ce mafaka ta farko mai aminci ga musulmai, kuma Sarkin Habasha, Najashi, ya ba su 'yanci da tsaro wajen gudanar da ibadunsu da kuma aiki da hukunce-hukuncen addininsu. Wannan kuwa ya sanya Afirka ta kasance tana da fifikon tarihi wajen karɓar da'awar Musulunci a farkon shekarun samuwarta.
Shehin malamin ya kuma bayyana cewa dangantakar Afirka da Musulunci ba ta tsaya ga hijirar Habasha kaɗai ba, a'a, tana bayyana a cikin fitattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina al'ummar Musulunci ta farko. Daga cikinsu akwai Sayyida Māriyah al-Qibɗiyyah, matar Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Alihi) kuma mahaifiyar ɗansa Ibrahim; Ummu Ayman al-Nūbiyyah daga ƙasar Nubia (Sudan), wadda ta kasance mai renonsa da kuma mai yi masa hidima; da kuma Bilal al-Habashi, ladan Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Alihi), wanda ya ci gaba da kasancewa mai tsayin daka kan wilayar Ahlul Baiti (a.s.). Ya bayyana cewa waɗannan alaƙoƙi da dangantaka suna ɗora wa 'ya'yan nahiyar Afirka nauyi mafi girma na ci gaba da ɗaukar saƙon Musulunci.
Kuma Shehin malamin ya bayyana cewa kira zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki wajibi ne a kan dukkan muminai, yana kafa hujja da faɗin Allah Ta'ala:
"Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka."
Ya bayyana cewa cikakkiyar ma'anar wannan tafarki ita ce riƙo da wilayar Ahlul Baiti (a.s.), domin su ne hanyar samun yardar Allah Maɗaukakin Sarki, kamar yadda ya zo cikin addu'o'i da ruwayoyi masu daraja:
"Su ne suka kasance hanyar zuwa gare Ka, kuma tafarkin isa ga yardarka."
Ya kuma bayyana cewa Afirka tana da babban shiri da karɓuwa ga koyarwar Makarantar Ahlul Baiti (a.s.). Ya nuna cewa Musulunci ya bazu daga Afirka zuwa Turai ta hanyar Andalus, kuma al'ummomin Afirka sun tarar da Musulunci a matsayin tsari da ke tabbatar da adalci, mutuncin ɗan Adam, da kare haƙƙin bil'adama, har ma da haƙƙin dukkan halittu.
Ya jaddada cewa ɗan Adam a yau yana neman mafita ga matsalolinsa na tunani, zamantakewa da ɗabi'a, kuma Musulunci na asali shi ne kaɗai yake da ikon gabatar da irin waɗannan mafita. Ya kafa hujja da maganar Imam Ja'afar al-Sadiq (a.s.):
"Da mutane za su san kyawawan maganganunmu, da sun bi mu."
Sannan ya yi kira da a inganta hanyoyin gabatar da Musulunci tare da isar da sahihin surarsa ga duniya. Haka kuma ya jaddada muhimmancin amfani da kafafen sadarwar zamani da sabbin fasahohi wajen yaɗa ilimin Musulunci da koyarwar Ahlul Baiti (a.s.), yana mai bayyana cewa waɗannan hanyoyi sun buɗe manyan damammaki na wa'azi da ba su kasance a hannun al'ummomin da suka gabata ba, lamarin da ke ƙara girman alhakin masu aikin tablighi.
A wani ɓangaren kuma, Shehin malamin ya ƙarfafa wa ɗaliban Hauza gwiwa da su yi amfani da rayuwarsu wajen neman ilimi da aikata ayyukan ƙwarai, tare da tsara abubuwan da suka fi muhimmanci bisa abin da zai jawo yardar Allah Maɗaukakin Sarki.

Ya kuma tabbatar da cewa alhakin ɗalibai mata na ilimin addini bai gaza na maza muhimmanci ba, kuma ma yana iya zama mafi girma saboda irin buƙatar da al'ummomin mata suke da ita ga shiriya da ilimantarwa.
A ƙarshe, ya yaba da ikhlasi da ƙwazon da ɗaliban Afirka suke nunawa, musamman yadda suke dagewa wajen koyon harshen Larabci kafin shiga Hauzar Ilimi. Ya bayyana cewa wannan babban mataki ne mai cancantar yabo, domin yana taimakawa wajen fahimtar Alƙur'ani Mai Girma da kuma ilimin Ahlul Baiti (a.s.), tare da isar da saƙonsu zuwa ga al'ummominsu.
WAHA HAUSA (Labaran hauzar Najaf al-ashraf)
https://t.me

An karɓo daga Imam Ja'afar as-Sadiƙ (a.s) cewa:
"Ba na son in ga matashin cikinku sai yana cikin ɗaya daga cikin waɗannan halaye biyu: ko dai malami ne, ko kuma mai neman ilimi. Idan bai kasance haka ba, to ya yi sakaci. Idan ya yi sakaci, ya yi asara. Idan ya yi asara, ya aikata zunubi. Idan kuma ya aikata zunubi, makomarsa ita ce wuta. Na rantse da Wanda Ya aiko Annabi Muhammad (s.a.w.a.) da gaskiya."
Madogara: Amāli Na Sheikhuɗ-Ɗusy (r.a), shafi na 303, hadisi na 604.
A wannan hadisin Imam Ja'afar as-Sadiƙ (a.s) yana zaburar da matasa su domin su tashi tsaye wajen neman ilimi da yaɗa shi. Matashi ko dai ya zama malami, idan Allah Ya ba shi wannan baiwa, ko kuma ta zama mai neman ilimi, musamman ilimin addini. Domin wanda bai tashi ya nemi ilimin addini ba ta yaya zai bauta wa Allah (swt) ingantacciyar bauta? alhali bai san Shi ba, bai san abinda yai umarni ayi ba da kuma abinda ya hana.
In matashi yai sakaci da neman ilimi, sakacin na iya kai shi ga asara. Asarar kuma na iya jefa shi cikin zunubi, hakan kuma ya kai shi ga mummunar makoma (Allah ya kiyashe mu).
Wannan shi ya sa Imam (a.s) ya yi wannan gargaɗi mai tsanani, domin ya zaburar da matasa su yi amfani da ƙuruciyarsu wajen neman ilimi da kusantar Allah maɗaukakin sarki tun suna ƙananun su.

Muna taya Imamin wannan zamanin da malamanmu masu girma da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya bisa tunawa da ranar haihuwar Jagoran Halittu Annabi Muhammad s.a.w da Jikanshi Imam Ja'afarus Sadiƙ a.s.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya azurta mu da ziyararsu a duniya da cetonsu a lahira.
اللهم صل على محمد وآل محمد وعجل فرجهم ياكريم
WAHA HAUSA (Labaran hauzar Najaf al-ashraf)
https://t.me
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya azurta mu da ziyararsu a duniya da cetonsu a lahira.
اللهم صل على محمد وآل محمد وعجل فرجهم ياكريم
WAHA HAUSA (Labaran hauzar Najaf al-ashraf)
https://t.me
WAHA HAUSA (Labaran hauzar Najaf al-ashraf)
Photo
Muhawarar Imam Ja'afarus-Sadiƙ (a.s) da Abu Hanifa A Kan Rushe Ƙiyasi...!
Abu Hanifa ya shiga wurin Imam Ja'afar bn Muhammad as-Sadiƙ (a.s). Sai Imam (a.s) ya ce masa:
«"Ya Aba Hanifa! Na ji cewa kana yin ƙiyasi a cikin addini?"»
(Anan ƙiyasi shi ne a kwatanta wani al'amari da aka san hukuncinsa a shari'a da wani al'amari makamancinsa wanda ba a sami nassi ko hukunci kai tsaye a kansa ba, sannan a ba su hukunci ɗaya saboda irin kamanceceniyar da ake ganin a tsakaninsu.)
Ya ce: "Eh."
Sai Imam (a.s) ya ce:
«"Kada ka yi ƙiyasi. Domin wanda ya fara yin ƙiyasi shi ne Iblis, lokacin da ya ce: 'Ka halicce ni daga wuta, kuma Ka halicce shi daga laka.' Sai ya kwatanta wuta da laka. Da ace ya kwatanta hasken Adam da hasken wuta, da ya san girman banbancin da ke tsakaninsu."»
Sannan Imam (a.s) ya tambaye shi:
«"A wurin Allah wanne laifi ne ya fi girma: kisa ko zina?"»
Ya ce:
«"Kisa."»
Sai Imam (a.s) ya ce:
«"To me ya sa Allah Ya yarda a tabbatar da kisa da shaidu biyu, amma bai yarda a tabbatar da zina ba sai da shaidu huɗu?"»
Sannan ya sake tambayarsa:
«"Wanne ya fi falala: sallah ko azumi?"»
Ya ce:
«"Sallah."»
Sai Imam (a.s) ya ce:
«"To me ya sa mace mai haila take rama azumi amma ba ta rama sallah? To ta yaya ƙiyasinka zai tsaya? Ka ji tsoron Allah, kada ka yi ƙiyasi."»
Sannan ya tambaye shi:
«"Fitsari ne ya fi ƙazanta ko maniyyi?"»
Ya ce:
«"Fitsari."»
Sai Imam (a.s) ya ce:
«"A kan ƙiyasinka, ya kamata wankan janaba ya wajaba saboda fitsari ba saboda maniyyi ba. Alhali Allah Ya wajabta wanka saboda maniyyi, bai wajabta shi saboda fitsari ba."»
Haka kuma Imam Ja'afar as-Sadiq (a.s) ya ce:
«"Masu yin ƙiyasi sun nemi ilimi ta hanyar ƙiyasi, amma ƙiyasin bai ƙara musu komai ba face nisanta su daga gaskiya. Lalle addinin Allah ba a samun sa ta hanyar ƙiyasi."»
A wata riwayar Imam a.s ya ce wa Aban bin Taghlib:
«"Ba a auna Sunnar Manzon Allah da ƙiyasi. Ashe ba ka ga cewa mace mai haila tana rama azumi amma ba ta rama sallah ba? Ya Aban! Idan aka fara auna Sunnah da ƙiyasi, addini zai lalace."»
---
Madogara
1. Al-Kafi, na Sheikhul-Kulaini, Kitab Fadlil-'Ilm, Babin: al-Bida' wa ar-Ra'y wa al-Maqayis.
2. 'Ilalush-Sharā'i', na Sheikhus-Saduƙ, babin dalilin haramcin ƙiyasi da muhawarar Imam Ja'afar as-Sadiƙ (a.s) da Abu Hanifa.

❤1
An rawaito daga Imamul-Mahdi (a.j):
"Lalle ba mu yi sakaci wajen kula da al'amuranku ba, kuma ba mu manta da ambatonku ba. Ba dan haka ba, da tsananin bala'o'i sun sauko muku, kuma da maƙiyanku sun hallaka ku gaba ɗaya. Saboda haka ku ji tsoron Allah Mai Girma da Ɗaukaka, kuma ku taimaka mana."
Madogara: Biḥār al-Anwār.

Tsarin Lokacin Rayuwar Yau Da Kullum!.....
An ruwaito daga Imam Musa al-Kaiim (a.s) cewa:
"Ku yi ƙoƙari ku raba lokacinku zuwa kashi huɗu:
1. Wani yanki na lokaci domin ganawa da Allah ta hanyar ibada da munajati (zance na sirri da Ubangiji).
2. Wani yanki na lokaci domin neman abin masarufi da gudanar da rayuwa.
3. Wani yanki na lokaci domin zama tare da 'yan'uwa amintattu, waɗanda suke nuna muku kurakuranku, kuma suke yi muku nasiha da zuciya ɗaya ba tare da munafunci ba.
4. Wani yanki na lokaci kuma ku keɓe shi domin abubuwan jin daɗinku(nishaɗinku) wanda ba na haram ba. Domin da wannan lokacin ne za ku sami ƙarfi da kuzarin gudanar da sauran lokutan uku."
Madogara: Littafin Tuhaful-Uƙul ʿan Ālir-Rasūl, na Shaikh Ibn Shuʿbah al-Ḥarrani (ɗaya daga malaman ƙarni na huɗu bayan hijira), shafi na 409, a babin: "Wa'azozin Imam Mūsā bn Jaʿfar al-Kāẓim (a.s) da hikimominsa."

Daga Hasken Alƙur'ani mai girma!
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka mayar da ni (duniya), domin in aikata ayyukan ƙwarai."
Tuba mai amfani ita ce wadda take faruwa tun a lokacin da mutum yake cikin lokacin da ya ke da zaɓi, kuma ta haifar da sauyi a ɗabi'a, mayar da haƙƙoƙin waɗanda aka zalunta, da kuma gyara abin da mutum ya lalata.
Amma nadama bayan mutum ya rasa ikon gyara ko yin aiki, ba komai ba ce face nuna baƙin ciki da takaici kan sakamakon saɓo. Wato wani yanayi ne na zuciya kawai, ba wani matsayi na zaɓi da nufi ba wanda zai iya canja makomar mutum.
Marja'in Addini Sheikh Muhammad al-Ya'aƙubi (Allah Ya ƙara ɗaukaka darajarsa).
26 Rabī'ul Awwal 1448 AH / 9 Satumba 2026.

Daga cikin manyan alamomin hikima a cikin halayen mutum akwai iya sarrafa harshensa da kuma riƙo da magana madaidaiciya. Saboda haka, ya wajaba mutum ya yi amfani da hikima yayin magana da mu'amala da sauran mutane.
Kalma ba sauti ne kawai da ke wucewa ba; a'a, tana da nauyi da alhakin da zai iya gina dangantaka ko ya rushe ta, ta buɗe ƙofofin alheri, ko kuma ta sa mai faɗinta ya yi nadama.
Sheikh Hassan Al-Saffar

An ruwaito daga Imam Al- Hasan al-Askari (A.S.) cewa ya cewa ƴan shi'arsa
Ina yi muku wasiyya da tsoron Allah, da Aikata tsantseni A ci cikin addininku, da ƙoƙari domin Allah, da gaskiya a zance , da mayar da amana ga duk wanda ya ba ku ita, ko mutumin kirki ne ko fajiri. Haka kuma ina yi muku wasiyya da yawaita sujada da kyautata maƙwabtaka.
Da waɗannan kyawawan halaye ne Annabi Muhammad (S.A.W.A.) ya zo.
Ku yi salla tare da mutanen da kuke zaune a cikinsu, ku halarci jana'izarsu, ku ziyarci marasa lafiyarsu, kuma ku sauke haƙƙoƙinsu.
Domin idan mutum daga cikinku ya kasance mai kiyaye addininsa, mai gaskiya a maganarsa, mai sauke amana, kuma mai kyautata ɗabi'arsa ga mutane, za a ce: “Wannan ɗan Shi'a ne.” Wannan kuwa yana faranta mini rai.
Ku ji tsoron Allah, ku kasance abin ƙawatawa gatemu, kada ku kasance abin ƙyama.
Ku jawo mana dukkan soyayya da ƙauna, kuma ku kore mana duk wani abu mummuna.
📚 (تحف العقول)

Allahu Akbar ba tana nufin Allah yafi komi girma bane, inkace yafi komi girma kabashi ƙiyasi.
An karɓo daga Imam Ja’afar al-Sadiq (A.S.), ya ce:
Wani mutum yana wurinsa ya ce: «اللَّهُ أَكْبَرُ» (Allah ne Mafi Girma).
Sai Imam (A.S.) ya tambaye shi: “Allah Ya fi girman mene?”
Mutumin ya ce: “Ya fi komai girma.”
Sai Abu Abdillah (Imam Ja’afar al-Sadiq A.S.) ya ce: “Ka sanya masa iyaka kenan!”
Mutumin ya tambaya: “To, yaya zan faɗa?”
Imam (A.S.) ya ce:
«قُلْ: اللَّهُ أَكْبَرُ مِنْ أَنْ يُوصَفَ»
Ka ce: “Allah Ya fi ƙarfin a iya siffanta Shi.”
Ma’anar ilimi
Wannan hadisi yana koyar da mu cewa girman Allah ba irin girman abubuwan halitta ba ne. Idan aka ce Allah Ya fi komai girma ta hanyar kwatanta Shi da wasu abubuwa, ana iya fahimtar cewa ana auna girmanSa da girman waɗannan abubuwa.
Amma Allah Maɗaukaki Ya fi ƙarfin duk wata siffa da tunanin ɗan Adam zai iya kewayewa . Saboda haka, ma’anar Allahu Akbar a nan ita ce: Allah Ya fi ƙarfin a iya bayyana ainihin girmansa da cikakkiyar siffa.
الكافي📚

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Bayani Game da Hana Sanya Hijabi a Makarantun Azerbaijan
A Ranar kamun kai da Kunya ta Duniya (Yawm al-Afaf), wacce aka zaba domin ta dace da ranar haihuwar Sayyida Zainab, ‘yar Amirul Muminina Ali (a.s), shugabar mata masu kamun kai ta farko bayan mahaifiyarta Fatimah Al-Zahra (a.s),
muna bayyana bacin rai da tsananin bakin ciki da kuma fushin mu game da yanke hukunci da gwamnatin Azerbaijan ta yi na hana daliban da ke sanya hijabi halartar makarantu, da kuma hana su damar samun ilimi wanda hakki ne na shari'a ga kowane dan kasa.
An fitar da su daga azuzuwan su da karfi yayin da suke zubar da hawaye cikin bakin ciki , a yayin da ‘yan uwan su dalibai suka shiga damuwa da bakin ciki,
suka tsaya cike da mamaki a kofofin makarantun, suna kallon cibiyar ilimi mai cike da aminci da aka hana su, cikin bakin ciki da yanke kauna .
Wataƙila hukuncin ya shafi malaman da ke sanya hijabi ma, to wane laifi suka aikata da za a azabtar da su?,
Kuma idan hujjar ita ce manufar tsarin mulkin kasa na rashin alaka da addini, shin (al,maniyanci) na nufin sace ‘yancin jama’a da hana bin addinin mafiya rinjiyen jama’ar Azerbaijan ne? Domin hijabi ba sabon abu ba ne ko bako a can har a hana shi, akasin haka,
an ruwaito a cikin ingantacciyar hadisi cewa: (kamun kai ita ce kan dukkan alheri).
Kuma ina ganin Shugaban Jamhuriyar Azerbaijan ya ga wadannan abubuwan masu ban tsoro da ke sosa zuciyar kowane uba mai tausayi da jin kai kuma wanda bai yarda da hakan ga ‘ya’yansa ba.
Watakila hukuncin bai fito fili ba game da wannan matakin, sai dai shugabannin makarantun ne suka fassara shi a haka, kuma a lokacin dole ne a hukunta su kan wannan babban laifi. Shugaban uba ne ga dukkan wanda yake mulka,
Yana daga cikin mafi muhimmancin wasiyoyin Manzo (S.A.W) ga Amirul Muminina Ali (a.s) cewa ya zama uba ga al’umma, domin uban-taka shine mafi muhimmancin halayen shugaba mai nasara. Ya ce masa: (Ya Ali, ni da kai ne ubanni ne na wannan al'umma). Kuma sunan shugaba Aliyef an ciro shi ne daga sunan Amirul Muminina Ali (a.s), to ya kamata ya dauki wannan kyakykyawan hali daga gare shi. Kuma wadannan daliban da ke sanya hijabi ‘ya’yan shugabar matan talikai Fatimah Al-Zahra (a.s) ne masu tafiya a kan hanyarta, don haka kada ku sanya bacin rai a cikin zukatan su masu tsarki,
Musulmai sun ki amincewa da irin wannan qarari lokacin da ta fito daga wata kasa dake yankin Turai da aka sani da gaba da Musulunci, to ta yaya za su yarda da ita a wata kasa da kason Musulmai a cikinta ya kai kashi 96%?
Maguzanci a fage daban-daban ita ce manufar gwagwarmayar da shaidan da mataimakan sa cikin mutane suka kalubalanci ‘yan adam da ita tun farkon halitta. Don haka ya yi wa Adamu (a.s) da Hawwa'u rada har suka ci daga itaciyar da aka haramta domin su cire musu iffar su . Allah Ta’ala Ya ce: ( Sai Shaiɗan ya yi musu waswasi domin ya bayyana musu abin da aka ɓoye musu daga al'aurorinsu..) (Al-A'raf: 20).
▪ Allah ya Kuma cewa : (Yana cire musu tufafinsu domin ya nuna musu al'aurarsu) (Al-A'raf: 27).
▪ Kuma Ya ce: (bayan sun dandana yayan itatuwan,sai al'aurarsu ta bayyana a gare su) (Al-A'raf: 22).
Saboda haka, muna ganin cewa gyara wannan shawara da komawa daga gare ta ba shi da wani aibu ko wulakanci, a'a barima jarumtaka ne da kuma matsayi na hikima da ke kawar da fushin al'umma..